Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: Yadda aka kama wani shugaban makaranta yayi lalata da yara 7

Ana Zargi wani shugaba wata makaranta da yin lalata da wasu dalibai guda bakwai a kwara

Advertising

Wani Rikici Ya biyo bayan zargin lalata da dalibai Guda Bakwai da ake yi wa Shugaban ta Kwalejin Musulunci Hassanat da ke llori a Jihar Kwara.

Wasu kafafen Yada labarai sun rawaito cewa shugaban mai suna Samuel Prosper ya buya, tare da rokon a yafe masa akan abin da ya aikata.

To sai dai binciken Aminiya ya nuna a ranar Alhamis gwamnati ta rufe makarantar, sai dai zanga-zangar shugabbaninta Ma’aikatar Ilimi sake bude ta. ya sanya Wata maaikaciuya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce duk da shugaban da ake zargi ya ajiye aiki, makaranatar ba ta da dalibai masu sunyaen da kafafen yada labarai suka rawaito a makaranatar.

Advertising

Ta ce kafin wannan lokacin, shugaban makaranatar ya sha korafin ana yi wa rayuwarsa musamman kasancewarsa Kirista da ke jagorantar makaranatar Musulmi mai zaman kanta barazana.

“Shi kuma shugaban riko ne, kasancewar tsohuwar shugabar ta samu wani aikin a Abuja.

“Da yake shi ne mataimakinta, sai aka ba shi kafin zabar wani sabon shugaban kuma ana tsaka da haka ne mai makarantar ya rasu,” in ji ta.

Wata Mojirayo, ta ce, “Ba mu taba jin wannan labarin ba sai yau da safe.”

Har ila yau, kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce babu wani dan jarida da ya tabbatar wa faruwar lamarin.

“Abin da na ce shi ne babu wanda ya shigar da korafi makamncin wannan ofishinmu,” in ji shi.

A nasa bangaren, kakain ma’aikatar ilimi ta jihar, Peter Amongbonjaye, ya ce ba shi da hurumin yin magana kan lamarin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button