Advertising
Advertising
Labarai

Bidiyon wani hamshakin dan kasuwan Abuja ya yiwa mai Goge-Goge dukan kawo wuka sabida ta nemi hakkin ta.

Nelson Fitaccen dan kasuwa a garin Abuja Nigeria An dake shi yana dukan wata mai aikin goge goge (cleaner) Saboda ta nemi ya bata albashin ta.

Advertising

An bayyana cewa budurwar mai suna precious an bata kwangila tsaftar gidan da Nelson ya gina haka kuma ta nemi ya biyata kudin aiki ₦130,000 ya kuma yarda zai biya.

Precious tace a dai dai lokacin da aka kusa kammala wannan aiki taje gurin Nelson domin ya bata rabi a cikin kudin aikin saboda ta sallami wanda suka taya ta aikin.

https://www.instagram.com/reel/CidNSPJok71/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

A cewar rahoton na Sapele Matters, Nelson ya ki biyan ma’aikacin Hakkin ta ya kuma gargadeta data fitar masa a gida, precious taki fita daga gidan inda ya watsi da kayan aikin nata kuma ya hada mata da duka.

Advertising

An kama Nelson ne bayan an kai rahoto ga Hukumar ‘yan sanda, Sai dai daga baya aka sake su. Mai tsaftar ya yi zargin cewa a ofishin ‘yan sandan, dan kasuwar ya yi alfahari cewa zai yi amfani da kudinsa da kuma tasirinsa wajen cin nasara a wajen gudanar da shari’a.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button