Wani Abun kunya Ya Bayyana Bayan Mawaki Rarara ya Gama Rabon Motoci A Gasar wakar sa.
Wani Matashi dan garin jihar katsina Dan kauyen Rarara ida nan ce mahaifar mawaki Dauda Kahitu Rarara, Yayi wani roko ga gidan jaridan jaridar Rariya da su temaka su mika masa wani sako da yake son ya isa gurin mawakin.
Kauyensu Mawaki Rarara Na Fama Da Rashin Kyawun Hanya Da Sauran Abubuwan More Rayuwa.
Salam RARIYA ina muku fatan alkairi
Allah ya kara basira. Sunana Isah Aliyu Kahutu, karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.
Kamar yadda kuka sani Kahutu mahaifa ce ga sanannen mawakin siyasan nan Dauda Adamu Kahutu Rarara, amma a zahirin gaskiya ba mu san me ake cewa romon dimokuraɗiyya ba saboda duk wani cigaba na zamani bai yi mana ba.
Misali: ba mu da hanya, ba isassun malaman makaranta, ba malaman asibiti, Ba daukar ma’aikata. Haka kuma Matasan mu suna bukatar ayyukan yi.
Wannan wasikar ta fito ne bayan da mawakin ya gama rabon motoci da manyan wayoyi na gani na fada saka makon gasar wata wakar saai suna “Jagaba Shine Gaba”.
Don Allah (RARIYA) ku taimaka mana ku yada wannan babban al’amari.