Labaran Kannywood

Aminu Ala-Daga Rana Mai Maman Ta Yau Bazan Kara Yiwa Wani Dan Siyasa Waka Ba Matukar Ba A Jam’iyyar Mu Ta ADP Yake Ba.

Fitaccrn mawakin Hausa Aminu Ala, ya ce ba zai kara yi wa wani dan siyasa waka ba idan har ba dan jam’iyyarsu ta ADP ba.

A shekarun baya munyi wasa da damar mu amma yanzu na tsunduma cikin siyasa tsundum sabanin a baya, Saboda haka ba zan kara yi wa kowa wakar siaysa ba idan har ma dan jam’iyyarmu ba.

Fitaccen mawakin dai ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar dan majalisar tarayyar a karkashin jam’iyyar Action Democratic Party, (ADP) mai alamar littafi.

Hotuna a soshiyal midiya sun nuna Aminu Ala a jerin gwanon motoci na daga hannu a wani yanayi mai kama da na kamfe.

A yanzu dai a iya cewa da yawan jaruman fim fun wada harkar siyayasa ka’in da na’in, Dankuwa bayan mawaki ala akwai sauran mawaka da suka fito takara a wannan jam’iyar ta ADP, Kaman su Daddy Hikima wanda akafi sani da Abale.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button