Turkashi Yadda wani ɗa guda daya ya kashe iyayensa (Bidiyon).
Awani labari da muke samu An bayyana wani ɗa Guda da ake zargi da kashe iyayensa saka makon wata yar takadama da ta afku.
Wani matashi dan jihar Anambra wanda ake zargi da kashe iyayensa yana kwance a wani asibiti dake Nnewi bayan wanna zargi da akemasa.
Wani rahoto da yake fitowa ya bayyana matashin ya kashe iyayensa ne sakamakon wata zazzafar mahawara data faru tsakanin sa dashu saboda sunki bashi kudi.
A ranar Alhamis 22 ga watan satumba makwabtan gidan sun bayyana cewa sun ji wani wari ne yana fitowa daga gidan Sanadiyar datasa suka kutsaci domin ganin abinda ke faruwa.
Koda shigarsu sun bayyana cewa sunga gawarsu wadda har ta fara rubewa da yankan aduna a jikin su, An zarki dan nasu tilo wanda ake kira chukwudi ne ya kashe su kwanaki uku da suka wuce.
Matashin da ake zargi ance ya kammala katlratun digiri a wata jam’a dake jihar Anambra, an kuma bayyana cewa ya shahara wajen shan miyagun kwayoyi.
Kakakin Rundunar ’Yan sadan Jihar, DSP Ikenga Tochukwu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a 23 ga watan Satumba, ya ce rundunar ta kaddamar da farautar wanda ake zargin wanda a halin yanzu yake tsare.