Advertising
Advertising
Uncategory

Turkashi wani mutun ya ya ke marainansa a lokacin da yake bacci.

Wani manomi dan kasar Ghana ya tinci kansa a mawuyacin hali bayan da ya yanke marainan sa a lokacin da yake bacci.

Advertising

Manomin mai duna Atta ya bayyana yadda lamarin ya faru dashi a gadon asibiti, inda ya bayyana lokacin da likitoci suka taru domin ai masa aiki.

Atta ya bayyana cewar Har yanzu ba ai masa aiki ba sakamakon bashi da kudin da mota zata dauke shi ta kaishi babban asibitin koyarwa na anokye dake kumasi a Ghana saboda channe za ai masa babbar tiyata.

Mutumin ya ce, yana barcin da rana ne a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama a ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marainansa.

Advertising

Atta, ya ce abin ya ba shi mamaki kwarai domin har lokacin da wasu makwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya rika jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.

Ya kuma kara da cewa lamarin ya sameshi amma har aka kawoshi asibiti gani yake kaman a mafarki ne, Ya kuma bayyana bayan ya dawo hayyacin sa yay ta mamakin n yadda akai wannan abu ya faru.

A wani karin haske da likitoci sukayi sunce bayyana cewar akwa wata larura da ake kira (parasomnia) wanda mutun zai riga yin wasu abubuwa da zakayi baka cikin hayyacinka.

Larura takan jawo wa mutun wannan abubuwa yayin bacci, kifta ido ko kuma futsarin kwance da kotafiya ana surutu da sauran su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button