Advertising
Advertising
Labarai

Dalibin daya maida satifiket dinsa don a bashi 500 ya bayyan abinda tsofafin dalibai suka bashi.

Matashin mai suna Oludare Alaba ya fadi amfanin da kudin da aka bashi zai masa na siyan kayan MC wanda zai ringa hadawa da wasan barkwaci.

Advertising

Idan zaku iya tinawa a kwanan baya cikin watan Satumba mun kawo muku labarin wannan mutashi mai suna Oludare wanda ya kammala makarantar jami’ar fasaha Ladoke Akintola (LAUTECH).

Ya nemi makarantar da yayi, su karbi Satifiket finsa su bashi kudi Naira 500, Sai dai hukumar makarantar taki amincewa da kudirin sa. Saidai tsofafin dalibai sun sunyi kokari sun hada masa 500 din sun bashi.

Matashin ya wallafa a shafin sa na Facebook irin kayan da ya siya da kudin da tsofaffi daliban suka bashi, wanda zasu temaka masa wajen sana’ar sa ta (MC) da kuma wasan barkwacin.

Advertising

A cikin wani bidiyo da Alaba ya raba, an gan shi da kwamfutar da kananan kwalaye guda biyu masu dauke da wayar salula (TECNO Spark 9) da kuma wani abu da yayi kama da katin wutar lantarki.

Ya ci gaba da yaba wa dukkanin kafafen yada labarai da suka sanya bidiyon nasa ya rika yaduwa a yanar gizo, ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ba shi goyon baya kan abubuwan da suka faru, inda ya bayyana cewa shi jarumi ne, mai barkwanci

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button