Labarai

Wasu mutane suna so suga Aure na ya lalace- Mijin baturiya Sulaiman isa isa yayi bayani game da wannan batu.

Matashin daya Auri baturiya Sulaiman isa isa ya bayyana rashin jin dadinsa ga wasu mutane da suke son ganin soyayyar sa ta lalace.

Wani matashi dan shekara 24 a duniya mai suna Suleiman Isah panshekara wanda ya Auri wata Baturiya Amuruka mai suna Janine Sanchez Reimann, mai kimanin shekaru 48 ya ce mutane na son ganin Auren nasa ya lalace.

Idan zaku iya tunawa cewa ma’auratan sun yi Aure ne a ranar 13 ga Disamba, 2020, a unguwar Gasau Panshekara a jihar Kano Lokacin da suka tatauna da ita ta kafafen sada zumunta.

Matar sulaiman mai suna Janine a cikin kalamanta a lokacin da tazo kano, ta bayyana yadda Isah ya samu amincewar ta ta shafin Instagram har kum taji tana son Auren sa.

“Ya aika mani sako a shafina na Instagram yana cewa Hi. Ban amsa ba saboda na samu yan zamba da yawa yan kasar Nigeriya wannan dalilin yasa naki amsawa.

Amma akwai wani saurayi da yake turo min sako kuma Sulaiman ya san shi dan damfara ne don haka sai ya ce, “ka samu aiki ka daina zamba marasa laifi.” Don haka ina tsammanin kamar mutumin kirki ne. ” (kara karantawa anan)

A cewar Sulaiman, wasu sun ce ya koma kasar sa Nigeria idan batirin nasa ya kare.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook ya ce

“Ina mamakin mutanen da suke gaya mani cewa idan baturin ya ƙare, dole ne in dawo Kano in zauna.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button