Allahu Akbar tabbas kaji abinda ya faru da wannan matar da danta saika zubda hawaye.
Tabbas duk wanda yaji abinda ya faru da wannan matar da danta sai ya kusa zubda hawaye.
An yi wani matashi wanda ya gaji
da mahaifiyar shi domin ta tsufa, ya yanke hukunci ya je far da ita a cikin daji, bayan ya dauke ta ya nufi daji da ita, sai ta fahimci abinda yake nufi, daga nan sai ta fara tsinkar ganye tana jefarwa a hanyar, bayan sun isa dokan daji, sai ya jefar da ita ya juya zai koma gida.
Bayan ya juya sai ya rasa hanyar da zai bi ya koma gida, nan take sai Mahaifiyarshi ta kira shi tace ya kai da na, ka saki hanya, ka kama bin hanyar da duk kaga ganyen nan ita ce hanyar ka, zata kai ka har gida, ina gudun ka bace ka tozarta cikin wannan mugun dajin ba kowa kusa da kai.
Jin hakan sai ya dawo ya rungume Mahaifiyar shi yana kuka yana neman Gafarar ta.
Ya Allah ka Gafartawa Mahaifan mu ka basu Aljannar Firdausi, ka hada mu da su a cikin ta, ka Azurta mu da dagewa da yi ma su Addu’a da biyayya da ran su ko bayan sun mutu
Allah kahadamu dasu a, jannatul firdausi Don darajar Annabi Muhammad S.A.W ALLAH