Labaran Kannywood
Bazan iya fitowa a kwarto ba kokuma dan daudu ba cewar Jarumin Kannywood Nura Hussaini.
Fitaccen dan wasan Hausa a masana’antar kannywood Nura Hussaini ya bayyana cewa bazai taba iya fitowa a mastayin kwarto ba ko kuma dan daudu.
Jarumi Nura Hussaini ya bayyana haka a wata hira da yake da gidan jaridar BBC Hausa cikin wani shiri mai suna daga bakin mai ita.
Nura Hussaini ya kasance sannan dan wasa a masana’antar ta Kannywood wannda aka dade ana damawa dashi a masana’antar kazuwa yanzu da ya tsunduma cikin harkar siyasa.
Jarumin ya tashi gidan malamai wanda sanadiyar haka ne yasa bai shiga masanaantar fim kai tsayeba sai da ya nemi sahalewar iyayen sa.
Haka zalika Nura ya bayyana yadda akai ya fara fim din da yadda akai ya hadu da kamfanin shirya fim din Sarauniya duk a tsakanin shekara 1998 zuwa 1999.
Ga cikakkiyar hira.