Advertising
Advertising
Labarai

Asirin wata mace ya tonu bayan tayiwa yar Aikinta duka har tamutu takuma jefa gawartq cikin daji a jihar Anambra.

Rahoton ya bayyana cewar matar tawa yar aikin nata duka har takai da ta mutu ta kuma jefa gawarta cikin wani daji ba tare da sanin dalilin hakan ba.

Advertising

Hukumar hana safarar mutane ta Jihar Anambra NAPTIP ta kama wata mata da laifin kashe yar aikin ta.

An bayyana cewar matar ta lakadawa yar aikin duka har ta mutu a kan wani dalili da ba a bayyana ba sannan ta jefar da gawarta a wani daji.

Bayan jami’an Hukumar NAPTIP tayi taka matar ta garzaya dasu har inda ta jefa gawar yar aikin a ciki n daji.

Advertising

Matar datake bada labarin yadda lamarin ya faru a cikin wani faifan Bidiyon tace ta lakadawa yarin yar duka har ta fara jijiga daga bisani ta kaita asibiti, Sai dai likitoci sun tabbatar mata da ta mutu.

Cikin Bidiyon tayi magana cikin harshen Igbo inda ta bayyana kaman haka; Na lakada mata duka sai ta fara jijjiga don haka na kaita wani (asibiti). Da zuwan mu suka ce ta mutu, sai na jefar da gawarta cikin daji.

Cikin Bidiyon an ga gawar yar aikin a yashe a cikin ciyayi a dajin, Daga nan aka kai matar gidan yari domin girbar abin da ta shuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button