Advertising
Advertising
Labarai

Hukumar DSS ta Kama Sojan Nijeriya da ake zargi da taimakawa ‘Ya ta’adda a Abuja.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS sun kama Jami’in Tsaron Soja da aka ajiye yake aiki a Muhammadu Buhari Cantonment dake tungan maje cikin birnin tarayyar Abuja da zargin bada haya da kuma saida Bindigu wa masu Garkuwa da Mutane.

Advertising

An kama shine a makon daya gabata a wuraren dangoki park dake zuba tareda hadin gwuiwar Yan Bangan Sakai dake wannan wurin.

A bayanan rahoto Jami’in Tsaron Sojan ya bada hayar Bindiga wa masu Garkuwa da Mutane akan Kuɗi N300,000 awani Aikin da masu Garkuwa da Mutanen su kayi, awani Aikin kuma N200,000 a Kudin Hayar Bindiga guda daya.

A rashin sa’ar Jami’in Tsaron Sojan, Masu Garkuwa da Mutanen sun ambaci Sunan sa a matsayin mai basu Makami na Bindiga. Sun kira sa akan wata harkar Bindigun AK47 akan zasu siya N3,000,000 inda nan take ya yarda ya fada.

Advertising

Sunje inda sukayi yarjejeniyar haduwa a Zuba suka dauki matsaya, shi kuma ya taho a Motar sa domin basu Makaman ananne Jami’an Tsaron su kayi Wuf dashi. An samu Bindiga Kirar AK47 da kuma Bindiga Kirar Magazine Mai Cike da Harsasai Talatin a Motar sa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button