Advertising
Advertising
Labarai

Yadda aka samu gawarwakin wasu mutane da Ambaliyar ruwa tai gaba dasu a kwara.

Hukumar yan kwanan kwana sunyi nasara samo gawarwakin wasu mutane biyu da ambaliyar ruwa yay awan gaba dashu a Akerebiata da bangaren illorin a cikin jihar.

Advertising

Mista Hassan Adekunle shine mai magana da yawun hukumar ta kwana kwana ya bayyana cewa jami’an sun samu nasala samun gawar wasu mutun biyu da kuma mota kira Toyota Yaris.

Yadda ya shaida cewar lamarin ya faru ne a ranar juma’a inda yake cewa matafiyan sun biyo hanyar cikin dare a kokarin su na su ketare wannan gogi, inda anan ne ruwan yay awan gaba dasu ciki.

Kakakin ya ce mazauna yankin sun taka rawar gani wajen kokarin fito da wannan gawarwaki da kuma motar tasu daga cikin wannan kogi.

Advertising

Adekunle ya yi jan hankali mai karfi wajen wayar da kan matafiya hanya da su dena bin hanya a yayin da ake ruwa mai karfi domin gujewa afkuwar hakan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button