Ba a son raina nai Aure ina 13 ba cewar wata budurwa da akai wa Auren wuri a wani kauye.
Wata budurwa ta bayyana irin bata kashin da dauki ba dadi da akai da ita lokacin da akai mata Aure wurri a gidan su, kasan cewar tanabda kananan shekaru.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana ce domin wayar da kai game da ba su hakkokinsu da martaba su da kuma ba su kwarin gwiwa bisa gudunmawarsu ta fannonin rayuwa daban-daban.
Wata budurwa mai suna maryam Hassan ta bayyanawa gidan jaridar Aminiya Abin da ya faru da ita bayan an mata Auren wurri a gidan su kasan cewar a lokacin tana da kananan shekaru a lokacin.
Da take bayani akan Yadda Auren ya kasance tace; tace iyayenta sun mata Aure tana da shekaru 9 inda sai da tai shekaru 13 suka tare da mijin nata.
Ta kuma bayyana rashin jin dadinta a Auren kasancewar duk kawayenta suna gida suna watayawa ba ai musu Aure ba, bayan kaita gidan miji tana gudowa ta dawo gida akan cewar ita bazata zaunaba amma iyayenta suna kara mai da ita.
daga karshe dai iyayen matashin sunce bazasu iya ba kawai a raba Auren, Haka iyayenta suka bada kudin da mijin ya kashe wajen Auren ta.
Ta bayyana rashin son Auren wurri da kuma matsaltsalu da yake haifarwa.
Nafarko tace ba samun fagimtar juna da mai ji, haka kuma shekarunki sunyi kuruciya da yawa duk maganar da za’a gaya miki ba lallai kiji ta ba.