Advertising
Advertising
Labarai

Abin tausayi wani mutun ya saka gidan sa a kasuwa don biyan kudin fansar ‘ya’yan sa.

Abin tausayi wani mutun ya saka gidan sa a kasuwa don biyan kudin fansar ‘ya’yan sa.

Advertising

Wani mutum Lukman Aliyu, mazaunin unguwar Aseyori da ke yankin Alagbado a jihar Kwara ya fara sayar da kayansa domin tara Naira miliyan 8 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da ‘ya’yansa biyu Abdulkadir Lukman da Muhideen Lukman suka nema, bisani rashin haɗuwarne yasa ya Saka gidansa a Kasuwa.

Da farko dai masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 20, amma bayan tattaunawa da suka yi, sai suka ce wa Lukman ya kawo Naira miliyan 8 ko kuma ya rasa YaYansa guda biyu.

ALFIJIR HAUSA ta tattaro cewa Lukman ya sayar da motar sa akan kudi naira 1,500,000 sannan kuma ya nuna sha’awarsa ta siyar da gidansa domin karbar kuɗin fansa da masu garkuwa da mutane suka nema.

Advertising

Lukman ya sayar da motarsa akan kudi Naira miliyan 1.5 kuma ya samu karin Naira 500,000 daga wajen sa (Yan uwa da abokan arziki) domin ya zama naira miliyan biyu a yanzu.

Tunda masu garkuwa da mutane suka dage a kan Naira miliyan 8 ko kuma su kashe masa YaYansa, ba shi da wani zaɓi illa ya yanke shawarar sayar da gidansa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button