Wata yarinya mai shekaru 10 ta bayyana yadda zata zama likita duk da cewar hannayenta basa aiki.
Wata ’yarinya yar shekara goma, wadda aka haifa da lalurar rashin aiki da hanun ta baya yi, ta bayyana burinta na zama likita da kuma yadda take yi wajen yin rubut.
Yarin yar mai suna Fatima Wadda take zamanta a garin kaduna karamar hukumar sabon gari ta bayyana cewa duk lalurar da take fama da ita, bazata hanata tai duk wani abu da mai hannu zai ba.
Fatima tayi bayyanin yadda take yin kwaliya da saka hoda dama yadda take yi wajen cin abinci da ƙafafuwan ta.
Yarinyar ta kara shaidawa manema labaran gidan jaridar Aminiya cewa bata samun wata tsangwam aga abokan mu’amala ta na gida da makaranta.
“Burina a rayuwa shi ne, duk da cewa hannayena ba su yin aiki, amma ina son zama likita ni ma, domin in rika kula da marasa lafiya,” a cewarta.
Mahaifiyar fatima mai suna Amina Idris ta shaida cewa an haifeta ne a haka takuma girma ne da wannan lalura ta rashin aiki da hanunta bayayi.
Kamar yadda ta ce, “Ita ce ’yata ta biyar a jerin haihuwata kuma daga kanta ban sake haihuwa ba saboda mijina ya sake ni sakamakon cewa ya gaji da dawainiyar Fatima.
“Cikin bai wahalar da ni ba kamar sauran na ’yan uwanta, wajen haihuwa ne da nakuda kawai na dan fuskanci matsala, don haka sai a asibiti na haihu, ba kamar na sauran ’yan uwanta ba.