Advertising
Advertising
Labarai

Yadda asirin wani dan garuwa ya tonu bayan yayi lalata da matayen aure sama da 40.

wata unguwa da ake kira Fanshekara cikin garin kano, An samu wani iftilai na bullar ko bayyanar wani Murgujejen kato mai suna Rabe bakin makarho-baka barin shanya ta bushe kota uban waye saika kwasa.

Advertising

Shidai wannan saurayi ya dade yana gudanar da sana’ar sa ta ga ruwa, a inda ya ringa tafka ta’asa da 6arna ta karkashin kasa, ba tare da an gano shi ba. Har saida dubunsa ta cika, bayan ya jima yana more rayuwarsa ta hanyar yin lalata da matan aure da kuma yan mata.

Ga yadda abin ya kasance, kamar yadda shi da bakinsa bayan an kama shi ya zayyanawa hukuma.

Abun kuwa kamar haka yake-yayin da duk ya fita gudanar da sana’arsa ta saida ruwan to akwai hanyoyi guda biyu (2) da yake amfani da su.

Advertising

(1) Akwai wani kwalli wanda ake kira wai “KIFDAU” da yake sawa wanda indai aka sake mace tai arba da shi to kuwa magana ta kare. Musamman matan Aure idan suka kirashi zasu siya ruwa a wajensa yake amfani da wanan kwallin wajen yin amfani dashu.

(2) wato hanyar da yake amfani da ita ga yan mata, yana amfani da wani irin “CINGAM” wacce cikin yaudara yakan bawa su yan matan cingam din wacce da zarar sun tauna ta sun hadiye tofah aikin gama ya gama ciniki ya fada kenan.

Yanzu gaka dai wannan mutumi na gun yan Hisbah domin cigaba da bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button