Advertising
Advertising
Labarai

Wani matashi dan Jihar zamfara yayi Alkawarin Auren Muneerat Abdussalam duk da halin da tashiga na rashin lafaiya.

Wani matashi dan Jihar zamfara yayi Alkawarin Auren Muneerat Abdussalam duk da halin da tashiga na rashin lafaiya.

Advertising

A jiya talata 24 ga watan Oktoba wasu hotunan Muneerat Abdussalam suka bayyana a kafar sada zumunta wanda take neman taimakon mutane bisa lalura rashin lafiya data sameta.

Muneerat ta kasance mai siyar da maganin mata kuma ta shahara wajen yin batsa a duk wata kafa ta sada zumunta da mutane ke amfani da ita, musamman ma kafar YouTube da Facebook.

Ta bayyana hotunan ta jiya gami da saka lambar akawun, ta kuma nemi taimakon mutane a game da rashin lafiyar da take damun ta.

Advertising

A jiya wani Matashi Dan Asalin Jihar Zamfara Mai Suna Anas Villa, Yayi Alkawarin Auren Muneerat Abdulsalam Indai Har Zata Amince Da Hakan

Matashin ya wallafa hakan a shafin sa Cewa: Ni dan asalin jahar Zamfara ne: na kuma shirya tsaf tare da tsarkake niya, domin mu rufawa juna asiri akan auran Muneerat Abdulsalam Tare da biyan sadaki kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button