Malan Ali na kwana Chasa’in ya maka Dan jarida a kotu bisa zargin sa da bata masa suna akan neman mata
Malam Ali na kwana Chasa’in ya maka Dan jarida a kotu bisa zargin sa da bata masa suna akan neman mata
Fitaccen jarumin nan a Masana’antar Kannywood Sahir Abdul Ya maka wani matashin dan jarida me suna Indabawa Aliyu imam a gaban kotu tare dashi da Jaridar daily news Hausa.
Jaridar ta daily news hausa ta ruwaito labarin data wallafa cewa Yan Mata Ku Yi Hattara Da Malam Alin na shirin Kwana Casa’in, Domin Rikakken Mazi*naci ne Cewar Wata Budurwa.
Wata matashiya a jihar Kano ta gargadi mata ‘yan uwanta da karsu kuskura suyi mu’amala da Jarumin Kannywood Sahir Abdul wanda aka fi sani da ‘Malam Ali Na Kwana Casa’in’ tana mai cewa rikakken mazi*naci ne.
Wannan labari ya bayyana a satin daya gabata inda ya karade kafar sada zumunta da sauran gidajen yada labarai.