Labaran Kannywood

Wasu Bidiyon Jarumar Kannywood Rahama Sadau Sun tada cece kuce a kafar sada zumunta.

Jarumar nan da ta shara a Kannywood da kuma Nollywood Rahama Sadau ta bayyana a cikin wani fefen bidiyo a cikin shiga ta irin mutanen kudu, kamar yadda majiyar mu ta ci karo da bidiyon, mun lura ta dauke shi ne a wajen wani shiri da suke shirin dauka a kudancin Najeriya wato Nigerian Film a turance.

Bayan wanda ya kai jarumar harta fara taka rawa a finafinan kudun Uzee Usman ya wallafa bidiyon a shafin sa na Tiktok,mutane da dama sun kalubalanci jarumar duba da yanayin shigar datayi duk da ba’a garin Hausawa akayi bidiyon ba.

Amma abunda mutane sukafi fadi shine bai kamata ace tana Bahaushiya kuma musulma tana irin wannan shigar mai matukar muni kuma ta sabawa Al’adar Malam Bahaushe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button