Advertising
Advertising
Uncategory

Nima bazan dau wulakancin yan sosiyal midiya ba marasa tarbiya cewar mansura Isa.

Tsohuwar jaruma a masana’antar kannywood mansura isa tayi magana a shafin ta na Instagram inda ta dora wani rubutu da tai da Turanci

Advertising

A wannan makon dai muhawara ta Barke kan shari’ar da ake yi tsakanin matar shugaban kasar da wani dalibin jami’a da ya fadi baƙar magana a kan ta a shafin Twitter.

Hausa Daily News ta fassara wannan rubutu kaman haka: “Kada wanda ya tambaye ni in ce wani abu a kan A’isha Buhari. Ni ma na taɓa shiga wannan halin. Haka ‘ya ta ma ta taɓa shiga irin wannan halin. Na ce a’a da cin mutuncin soshiyal midiya da kalaman ƙiyayya.

Ta kara da cewa Ni ba matar shugaban ƙasa ba ce. A matsayi na na ‘yar fim, na san yadda mu ke ji, inda wasu wawaye, marasa kunya, mahaukatan mutane, su kan zo kafar sadarwa, su na faɗin abubuwa a kan mu, su zage mu, su kira mu da sunaye marasa kyau.

Advertising

Wasu lokuta mu yi kuka a ɓoye. Manyan jaruman duniya da ba za su iya ɗauka ba, kan kashe kan su.

Ba zan kashe kai na ba, amma ba zan taɓa barin wanda ba shi da tarbiyyar gida ya yi wasa da rayuwa ta ko lafiya ta ba. Za su yi basaja da sunan ka, su ɗora bidiyon marasa lafiya a matsayin kai ne.

Wallahi, wallahi, abin da ciwo, har ta kai ƙarshe, na kai wasu marasa kunya gidan yari. Ba zan ɗaukar wa kai na ko iyali na ba. Kada ku taɓa ni, shi kenan.

Jarumar tayi bayani ne cikin fushi da bacin ran abin da akai wa matar shugaban kasan.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button