Yadda wani mutum ya lakadawa yarsa duka Har ta sheka barzau.
Turkashi yadda wani mutum ya lakadawa yarsa duka Har ta sheka barzau.
Yanzu Yaznu muke samun labarin Wani matashi mai shekara 25 mai suna Godsgift Uweghwerhen a ranar Larabar da ta gabata ya yi wa ‘yarsa mai shekaru uku bulala har lahira a unguwar Aladja da ke karamar hukumar Udu a jihar Delta.
Gidan jaridar ALFIJIR HAUSA, ta samu labarin cewa wanda ake zargin ya gudu ne bayan faruwar lamarin.
Sai dai jami’an banga na Aladja a unguwar Ubogo ne suka kama shi, aka mika shi ga Hukumar ‘Ƴan sanda a sashin Ovwian/Aladja.
An bayyana cewa mutumin ya kashe yarinyar ce saboda ta shiga gidan makwabcinsa.
Ya yi mata bulala tare da raunata ta wanda hakan yasa ta jima tana jinya kana tarasu daga baya.
Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, a wani sako da ya aika wa wakilinmu a Warri, a safiyar ranar Alhamis, ya ce, “sun tabbatar” tare da bayar da cikakken bayani daga bangaren ƴan sandan ba.
Ku cigaba da bibiyar mu Hausadailynews dan samun labaria masu inganci.