Advertising
Advertising
Labarai

Babbar Kotun tarayya ta Abuja ta amincewa “NDLEA” ta cigaba da tsare DCP Abba Kyari

Kotu ta amincewa "NDLEA" ta cigaba da tsare DCP Abba Kyari

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abujan dake kasar Najeriya ta bawa hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta “NDLEA” damar cigaba da tsare dan sanda “DCP Abba Kyari”, bayan ta kama shi kan zargin safarar hodar ibilis wato koken.

Advertising

Mai Shari’a Zainab Dimka Abubakar ita ta bada umarnin tsareshin bayan wata bukata da hukumar ta shigar da zimmar neman cigaba da tsare “DCP Kyari” da wasu mutum shida tsawon mako biyu.

Wadanda za’a cigaba da tsarewar su ne, DCP Abba Kyari, ACP Sunday J, Ubia, ASP James Bawa, Sufeto Simon Agirigba, Sufeto John Nuhu; Chibunna Patrick Umeibe, Emeka Alfonsus Ezenwanne, sanarwar da “NDLEA” ta fitar a ranar Talata inda tace.

Wanda ake zargi da safarar koken din na shida 6 dana bakwai 7 (Umeibe da Ezenwanne) sun amsa Iaifinsu cewa sun shigar da ita Najeriya ne daga Ethiopia.

Advertising

Ta kara da cewa, su kuma wadanda ake zargi na daya 1 zuwa na biyar 5 Kyari, Ubia, Bawa, Agirigba, Nuhu, ‘yan sanda ne da suka kama na shida 6 dana bakwai 7 kuma suka kai su “NDLEA” don yin bincike.

Sabida binciken da “NDLEA” ta gudanar ya nuna cewa, na daya 1 zuwa na biyar 5 sun ci amanar aiki kuma sun shiga an dama da su wajen safarar miyagun kwayoyi, da kuma saka hannu wajen Ialata hujja a kan masu Iaifi ta mua’amala da koken, a cewar sanarwar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button