Advertising
Advertising
Labarai

An Kama Wata Ƴar Damfara Mai Yin Ƙarya Da Juna Biyu Tana Satar Kaya A Manyan Kantuna

An kama wata budurwa da ake zargin tana yin amfani da ciki na bogi ta shiga kantunan Birnin Middelburg da ke ƙasar Afrika ta kudu tana sace kayan al’umma tana zubawa a cikin bogin domin ta tsira.

Advertising

Asirin wadda a ke zargin da a ka buƙaci a sakaya sunan ta ya tonu ne bayan da wani mai gadi ya ganta ƙuru-ƙuru kuma ya amshe kayan da ke hannun ta nan take kuma ya tona mata asiri.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi na can suna binkice domin gurfanar da ita gaban ƙuliya a ƙasar.

Wasu masu fadan ra’ayoyi sun ce wannan abu da tai ba wani abu bane illa talauci da yay tsamari a kasaken duniya.

Advertising

wasu kuwa zagin ta suke suna cewa ai dama bai kamata a ringa barin irin wannan mutanen kara zube ba, ba tare da ana gurfanar dasu gaban kotu ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button