Tabbas idan kaga hallitar yaran nan zaka tabbatar da Allah shine mafi girma da iko.
Tabbas idan kaga hallitar yaran nan zaka tabbatar da Allah shine mafi girma da iko.
Wannan yaran da kuke gani An haifesu ne mace da namiji wanda idan kun kalla da kyau zakuga cikin su a hade yake.
wannan yaran mun samu hotunan su a wani shafi mata suna BBCHAUSA.Ng wanda suka wallafa hotunan yaran mace da namiji suka kuma tabbatar da cewa an haifesu ne a haka kuma ana neman taimako domin a raba su
Sun bayyana cewa iyayen yaran ba masu hali bane basu da halin daukar nauyin yaran, domin ai musu aiki.
Haka zalika sun tabbatar da cewa; A tattaunawa da likitoci daban-daban a Burtaniya da Dubai (UAE), mun fahimci cewa Aikin Hassana da Hussaina ita ce irinta ta farko, kuma aikin tiyata don raba su zai ci sama da Miliyan 10; Inji su.
Sun kuma bayyana cewa Mahaifin wannan Yaran Talaka ne Dan Karamar Hukumar Giwa yana Zaune a Gangara Don Allah Darajar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ku taimaka Domin Raba wannan Bayin Allah Tabbas Mun San Halin da Ake ciki na Rashin Kudi da Tsadar Rayuwa a wannan Kasar Abin dai ba acewa komai Saidai Muce Alhamdulillah
Sun bayyana hakan ne duk a shafin B.B.C. HAUSA.Ng gami da dora Lambar akawun daga min tura kudaden temakon aikin.