Labaran Kannywood

Jerin hotunan Rahama Sadau da suka jawo mata cece kuce a shekara uku zuwa yanzu.

Fitacciyar jaruma a masana’antar kannywood Rahama Ibrahim Sadau wadda akewa lakabi da Rahama Sadau Yar asalin Garin Kaduna.

Jarumar ta kasance Fitacciyar a masana’antar kuma tana taka rawa daidai gwargwado kafin daga bisani tayi shigar banza da ta jawo ce-ce ku-ce a masana’antar.

A kwanan baya jarumar ta wallafa wasu hotunan ta a kafar sada zumunta ta twitter wanda mutane sukai ta cha chakar shigar da tai Hakan ya jawo wa wani kafiri yay batanci ga fiyayyen hallitta.

Wannan dalili yasa aka dakatar da jarumar daga fitowa a cikin fina finai.

Daga nan ne jarumar ta cigaba da wallafa hotunan banza duk sanda ranar zagowar haihuwar ta tai sai ta saki hotuna da suke jawo ce-ce ku-ce.

kaman yadda ta saki wasu a wannan karon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button