Wata sabuwa: Lilin Baba yayi magana Bayan yasir yace ya rabashi Da Ummi Rahab.
Yasir ya bayyana yadda aka yi unfollwing din sa daga shafin ummi din kuma ko ya kira mijin nata Lilin baba baya dauka bayan hidima da dawainiya da yayi da Ummi din tun tana yar karamar ta har ta kai matakin da takai ace na masa wannan sakayyar wanda hakan yasa shima unollowing din Lilin baban saboda ya fahimci kora da hali ake masa.
Kamar yadda muka yi muku alkawari cewa zamu jiyo ta bakin Lilin baba kan wannan batu lilin baba ya shaidawa tashar Tsakar gida cewa shi ba wani sabani da ya shiga Tsakanin sa da yasir sai dai in shi ya dauka da wani abu.
Game da batun korafin da yayi na rashin yin waya da Ummi da unfollowing din sa da aka yi kuma a shafin Ummi din Lilin baba ya bayyana wannan wani abu ne tsakanin ummi din da yasir, Babu hannun sa a ciki wani sabani suka samu da yasir din tun ana hidimar bikin wanda shi bai sani ba kuma yaso ya sulhunta tsakanin su da ummi bata bada dama ba.
A cewar lilin Baba in da wani abu a tsakanin sa da yasair ai bazai kira shi a waya video call ya hada shi da Ummin ba wanda sai da ya tsawatarwa Ummi din kafin ta yadda ma tayi magana da yasir din saboda tana fushi dashi, Kuma ba yau suka fara samun sabani suna shiryawa ba meyasa wannan karon zai dora laifin a kansa saboda yana auren ta ai bashi da damar tilasta mata sai ta kulashi musamman yanzu da take matar Aure.