Advertising
Advertising
Labarai

An bayyan yiwuwar Hukuncin kisa akan Malam Abduljabbar Nasiru Kabara

A cikin wata takardar da wani cikin tsoffin Lauyoyin dake tsaye ma Malam Abdul-Jabbar suka rubuta domin hutar da babban mai shari’ar dake kula da lamarij shari’ar, a cikin takardar sun tabbatar da hukuncin kisa akan ga abduljabbar din tare kuma da miƙa wa Alƙalin takardar domin ya karanta a bainar jama’a ranar Alhamis mai zuwa a matsayin hukuncin da ake yanke ma Malamin.

Advertising

A binciken Hausa Daily News ta bankaɗo abinda ke ciki. Takardar na dauke da rubutun furucin batanci da kalmomin da ake zargin Malamin ya furta a wancen lokacin, kuma ya amsa furta su din kamar yanda suka bayyana.

Kuma duk wanda ake zarga da furta wannan kalmomin, matukar ya amsa cewa ya furta su, to a kowane irin yanayi ya furta hukuncin kisa za’a zartar a kansa, kamar yanda manyan Lauyoyin suka bayyana a rubuce a takardar da aka karanta.

Lauyoyin masu gabatar da ƙara, masana shari’a tare da haɗin Gwuiwa da daya daga cikin tsoffin Lauyan Malamin ne suka zauna suka rubuta hukuncin domin gabatar wa ga mai shari’a.

Advertising

Sai dai a ɓangare guda kuma Almajiran Malam suna ta addu’ar zuwar wannan ranar tare da shirin gudanar da gagarumar zagaye a fadin Jihar ta Kano domin a cewar su a wannan ranar za’a saki Malamin nasu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button