Labaran Kannywood

An roki hukumar Hisbah dasu kama Abdul Babulaye akan wasu bidiyo da yayi na iskaci ya kuma dora a kafar sada zumunta.

An roki hukumar Hisbah dasu kama Abdul Babulaye akan wasu bidiyo da yayi na iskaci ya kuma dora a kafar sada zumunta.

Wani matashi mai suna Salisu Salisu ya roki hukumar Hisbah dasu kama Abdul Babulaye ko su taka masa burki akan iskancin da yake a kafar sada zumunta.

Matashin ya bayyana haka ne a shafinsa na sada zumunta inda yay subutu yake bayyana bacin ransa akan lamarin yakuma koka akan hukumar tace fina finai a game da lamarin.

Salisu yace: lokuta dama ana barin irin wadannan mutane suna aikata badai dai ba idon jama’a kuma ana kallon su sunayi baza ai magana ba ko kuma a sanarwa huku su dau mataki. Ya kara da cewa yakamata ace tun kafin iskancin sa yay karfi haka Hukumar tace fina finai ta dade da taka masa burki.

A karshen bayanin sa ya roki shugaban hukumar Hisbah dana tace fina finai dasu dakatar da yake aikatawa, ya kuma kara da cewa ba iya abdul Babulaye ba har da sauran masu aikata irin wannan iskancin a kafar sada zumunta.

Ya kuma yi addu’a allah ya shirya mana zuri’a ya karemu da irin wannan mugayen dabi’u Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button