Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta rabawa Mata ‘yan Kasuwa tallafin Naira Miliyan 60 “600M”

Gwamnatin Jihar Kaduna tace, kawo yanzu ta raba sama da Naira miliyan 600 ga mata ‘yan kasuwa ta hanyar asusun tallafawa mata da aka fara a shekarar 2018.

Advertising

Kwamishiniyar Aiyuka da cigaban Al’umma, Hafsat Baba ce ta bayyana hakan a wata
tattaunawa data yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN a ranar Alhamis a Kaduna.

Baba tace, an bayar da tallafin ne ga kungiyoyin mata ‘yan kasuwa a fadin jihar a matsayin lamuni mai sauki.

Tace, an kaddamar da asusun ne domin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu da kuma rage matsalolin wariyar jinsi a cikin harkokin kasuwanci.

Advertising

Har ila yau, don tallafa wa kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arzikin mata, wadanda suka riga sun shiga kasuwanci kuma zasu iya amfani da su don kara yawan jari, in ji ta.

Kwamishiniyar tace, kungiyoyin hadin gwiwa da kungiyoyin mata a karkara da birane zasu iya samun bashi na tsakanin Naira 5,000 zuwa Naira miliyan 10 ba tare da lamuni ba, domin samun kudaden da ake bukata sai kubi ta banki domin gaskiya da rikon amana.

A cewar Mrs Baba, akasarin wadanda suka ci
gajiyar tallafin na biyan bashin da suka karba,
Kwamishinan yace gwamnati ta sanya ido kan wadanda suka ci gajiyar shirin da kuma yadda suke gudanar da ayyukan su domin samin isassun labaran nasara da kuma koyan darasi.

A cewarta, ana cigaba da bayar da lamunin na shekarar 2022.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button