Labaran Kannywood
Hauka Yamin Rana cewar wani mai wasan barkwanci A TikTok bayan yaci mota a gasar da Rarara ya fitar.
Wani fitaccen dan wasan barkwanci a shafin TikTok ya bayyana yadda akai ya samu kyautar mota da kuma yadda ya samu kalu bale a game da hakan.
Matashin mai suna Mukhtar Yahaya wanda ake kira Da Babba comedy Ya bayyana cewa hauka yay masa rana bayan ya samu kyautar mota a gasar wakar da Mawaki Rarara yasa Ta Sha’abansharada.
Matashin yace; Da yawa mutane suna masa kallon mahaukaci, amma daya samu kyautar mota sai kowa yake sha’awar dama sune.
Anan ne yake cewa ko yanzu hauka ya masa rana tunda Gashi yaci kyautar mota.