Labarai

Yadda kungiyar Boko Haram ta kone wasu Runbun kayan abinci a Jihar Borno.

Wani mumunan hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai Jibwiwi na Karamar Hukumar Hawul a Jihar Borno, Inada suka kone rubunan abinci da kuma gidajen jama’a.

Rahotan ya bayyana yan Boko Haram din sun yaiwa kauyen kawanya ne a ranar Litinin da misallin karfe 6:00 na yamma.

Wani dan banga a kauyen ya ce

“Sun kone gidaje takwas da wani wajen ajiye kayan abinci; wanda da yawa masara, dawa da gyada aka ajiye a cikinsa. Daga nan sai suka wuce yankin Ngulde da ke Karamar Hukumar Askira, amma mun dakile su tare da taimakon mafarauta. Kai daukin da ’yan banga suka yi ya taimaka da a can ma barna mai tarin yawa za su yi,” inji shi.

Shugaban ’yan bangar yankin Arewa Maso Gabas, Shawulu Yohanna, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce sun dakile su don kada su sake kai wani hari wani yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button