DA DUMI DUMI: Dakata kaji labari mai dadi akan PI NETWORK.
PI NETWORK
A kalla kasuwannin Crypto wato Exchangers kusan guda 10 sukayi listing Pi Network tare da farashinsu, akwai wanda farashin Pi guda daya yake a Dalar Amurka 50, kimanin Naira dubu 35.
Abinda ya bawa kowa mamaki, saboda ana Pi closed mainnet ne, wata ana lokacin da Pi Core Team basu bada dama ayi kowace irin mu’amala da Pi ba.
Amma bamu sani ba ko akwai wata tattaunawa da yarjejeniya da Pi Core Team sukayi da wadannan exchangers din, na tabbata Pi Core Team zasuyi jawabi nan da kowani lokaci akan wannan sabon al’amari.
Na ga wadanda suka jima basa mining Pi duk sun dawo bayan sun ji labari Exchangers sunyi listing Pi.
Mun ce muku kuyi mining kun daukemu bamu san abinda mukeyi ba, har kuna zagin mu tare da yi mana habaici, tukunna ma kuka gani, sai an je Pi Open Mainnet, Pi Chainmall sunfara International transaction, Pioneers suna sayen kaya daga Kasar China ana aiko musu gida.
Mu kam ba abinda zamu ce game da Pi Network wanda ya wuce ALHAMDULILLAH 🙏