Ina Da Hujjoji Guda 10, Da Suka Sa Bazan Zabi Kwankwaso Da Yaran Saba, Haka Kuma Bana Ganin Laifin Wanda Zasu Zabe Shi Matukar Yana Da Hujja
Daga Abdulrahaman Sani Mai NangeBautar da tunani
kwankwaso yana bautar da tunanin magoya bayanshi, domin yana kawo wasu abubuwa na ruguza mutane, amma mun kasa fahimtar manufar shi, wanda 70% na manufar shi da muka gani a zahiri lokacin yana Governor a Kano, yana daya daga abin da ya kawo ci baya a garin Kano.
Rashin ganin girman masu Martaba : Ga dukkanin wani dalibin ilimi yasan cewa babu wani gari ko Kasa da zata bunkasa idan ba’a girmama MANYAN GARI,MALAM GARI,DATTAWAN GARI. Sanin kowa me cewa lokacin da Kwankwaso yana Governor a Kano babu mutum daya daga cikin wannan da ya bawa girman shi, kowanne gari yana bunkasa be idan akwai (discipline), wanda idan shugaba na wannan gari ya sauka daga manufar gari, sune wanda zasu tsawatar mishi. Amma lokacin da yake Governor an rasa wannan.
RASHIN ALQIBLA A ZAHIRI : kwankwaso bashi da tsayayyiar alqibla Domin yana da iyayen gida wanda suke juya shi, amma da yawan mutane basu san haka ba. Yana kokari sosai wajen biyawa iyayen gidan shi bukatar su, wanda wannan kowa yasan cewa makiyan wannab gari namu mai albarka ne. Misali kamar Olusegun Obasanjo, wanda yana daya daga cikin mutanen da suka karya Northern Nigeria wanda akwai mutanen da suke kallon shi a matsayin wanda ya gurgunta kasuwancin Jahar Kano da sauran abubuwa masu tarin yawa wanda baza su fadu a Wannan rubutu ba.
RASHIN BAWA TARBIYAR ADDINI MUHIMMANCI : kwankwaso shine founder na HIZBA a Kano, amma dole ce ta sanya shi. HIZBA ba tayi karfi ba sae da ya sauka 2003. Da Wani Governor ya zo kuwa yasan irin aikin da HIZBA tayi a Kano wajen tarbiya, lokacin da ya dawo 2011 HIZBA daga nan ta samu matsala, wanda da yasa kowa yasan HALIN da tarbiyar yaran Kano yanzu take. Idan da akwai tarbiya irin wadda mutanen Kano suka samu especially lokacin 2003 zuwa 2011, da har yanzu mustang Kano Masha’allah.
MATSALAR