Advertising
Advertising
Labarai

Abin Sha’awa: Bayan Shafe Shekaru 6 Suna Soyayya Yau Allah ya cika musu burin su sunyi Aure….

Bayan shafe shekara 6 Suna Soyayya Yau Dai Allah Ya Ƙaddara Auren Na Jidda da Jidda

Advertising

Wannan bawan Allah da kuke gani sunan sa Abdulmaji Bello dake Yolan Jihar Adamawa ita kuma sunan ta Hauwau Muhammad Inuwa yar asalin jihar Bauchi, daga lokacin da Allah ya haɗa su zuwa yau, a ƙalla sun shafe sama da shekaru 6 suna soyayya.

A cewar su sun sha gwagwarmaya da faɗi-tashi amma cikin ikon Allah ya ƙaddara zasuyi Aure.

A cewar abokin angon Adamu Yakubu Umar yace yayi mamakin masoyan da suka jima suna soyayya, ba tare da ɗaya ya guji ɗaya ba, har Auren su yazo, suna tare.

Advertising

Za’ayi auren ne ranar jumaar nan mai zuwa 13-01-2023 a Unguwar Fallelu dake Alkalerin Jihar Bauchi.

Muna rokon Allah ya basu zaman lafiya mai ɗorewa.

Wannan soyayya ta shekara 6 kafin Aure Allah ya ɗorar da ita har ƙarshen rayuwa

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button