Labarai

Falalalu ya fusata ya gayawa Shugaban kasa gaskiya akan Wahalar samun chanji.

Da CBN za tai duba da irin asara da mutane zasu tabka da an danyi kari akan wa’adin da aka bayar na carjin kudin nan. Da yawan mutane kusan har dare suke kaiwa a layin saka tsohon kudi su karbi sabo, mutanen karkara kuwa mafi yawan su ba su ma da Asusun ajiya a banki a haka suke kasuwanci da kudi a hannu.

Kurna maganar gaskiya Hanyar fadar sakon canja kudin da CBN tayi kadan, sannan wa’adin yayi kadan.

Ni na dauka in ana cikin matain tattalin arziki, Sassaukar mafita ake nemawa al’umma, ba kokarin jefa su cikin ukuba ba, bafa karamar asara za’a yi ba.

Ukuba irin wannan tana bukatar duba na tausayi da jinkai, domin kauda kai da kin kara lokacin, kai tsaye ya nuna, Gwamnati ta juya baya ga al’ummar da suka zabeta,

Kuma irin wannan halin shi ke haihuwar sababbin matsaloli, kuma ya jefa lyalai da yawa cikin tolauci, wasu ma daga hakan sun haukace kenan.

A shekarun baya a lokacin da President Muhammad buhan Yana mulkin soja, anyi canjin nan an baru labarin irin masifar da mutane suka shiga. Sannan ya faru kwanannan a Kasar Indian, har Yanzu mutanen kasar basu dawo hayyacinsu ba

Shugabanni su duba masalahar masu rauni cikin Al’ummarsu Shine adalci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button