Labarai

An ceto uwa da danta bayan kwana hudu acikin gini a girgizar kasar da akai a Turkey da siyria.

Wani baban abin mamaki daya faru shine na samun wata uwa da danta saban haihuwa da aka tono a cikin wansa gini ya danne a kasar Turkey da siyria.

gidan jaridar BBC ta rawaito to cewa yaron mai suna Yagis an tono shine a wani gini da ya rushe yayin girgizar kasar data afku.

Rahotanin da gidan jaridar kasar ta fitar sun bayyana cewa an ceto yaran cikin dare an kuma yi kokarin zaroshi a hankula inda daga bisani suka kai shi asibiti domin duba lafiyar sa.

jaridar ta bayyana cewa daga nin yaro yafita cikin koshin lafiya batare da an samu wani ciwo a jikin sa ba haka zalika itama uwar ta fita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button