Akwai Matsala Fa A Kano Muna Zaune Akan Bom Da Ka Iya Tashin kowa.
Daga Abdullahi Musa Sufi.
Yanzu wannnan matsalar ta fasa da kona ofisoshi, restaurants, sutudiyoyi, gidaje da sace sace har da raunuka da rasa rai a Jihar mu amma bama maganar magance abin nan?
Hidimar taya murna da zanga zanga kamar anfi basu muhimmanci kan jan hankalin juna don gyaran wannan lamari kuma hakan shine mafi alheri don kar a kara.
Yana da kyau gwamnati dake kai da mai zuwa su ji tsoron Allah su dau matakin gaggagwa wajen hada kai da kwararru a nemo bakin zaren ko da za’a ci gaba da muhawarar anci da zuwa kotu.
Maganar gaskiya abin da ya faru ya nuna muna kan time bomb da wallahi jagororin ma.basu fahimci girman qalubalen ba.
‘Yan gwagwarmaya ba sai an kira hotel ba ko zu mu zauna ko a bakin titi kan benci a karkashin bishiya don mu nemo maganin afkuwar haka gaba.
Jami’an tsaro mun yaba muku matuka amma gaskiya a wannan fannin na fitowar yan murnar cin zabe da masu laifin cikin su suka yi amfani da damar, akwai bukatar kara zage dantse.
Allah Ya wanzar da zaman lafiya a jihar Kano da Nijeriya baki daya Amin.