Labarai

Kalli yadda Wani Matashi ya labarta abin da abokin sa yay masa shida amaryar sa.

Muna cikin Shan ruwa Ina zaune akan kujera kusa da hajiya kawai sai jinayi message yashigo ta WhatsApp Ina dubawa sai Naga video ne wani abokina yaturo min. Sai nayi sauri nabude Ni Ina tinanin sakon barka da Shan ruwa ne.

Ina budewa Ashe videon kayan alatu ne suna Shan ruwa da amarya, Sai jinayi Yana cewa Allah sarki abokina wlhy tausayi kake bani. Allah sarki gwaro Allah ya aurar dakai abin tausayi.

Sai nayi sauri nayi minimizing sbd Ina kusa da umman mu banson taji Ashe tariga taji lokacin da ake cewa Allah sarki abin tausayi. Sai jinayi tana tambaya na waye Kuma abin tausayi??

Sai naji bazan iya boye Mata ba. Kawai nace wlhy hajiya wani Dan duniyan abokina ne yakemun iya hege Tayi dariya tace Allah sarki ai kowa da yanda Allah ya tsaro Mai Rayuwarsa,
Lokacinka Yana zuwa kaima Nan bada dadewa ba in Sha Allah,,. Sai naji wani mugun Dadi ya qumeni kaman infalla da mugun gudu,

Ya Allah kadauki Nauyinmu, Allah yaqara miki lpy hajjaju .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button