Turkashi an bankado saurayin da Rakiyya Moussa ke kuka akan sa.
Ana wata ga wata Wata jaruma a masana’antar Kannywood ta bayyana irin soyayyar ta da wani jarumi a masana’antar Kannywood wanda ta nuna bazata iya deba sonsa ba.
Fitacciyar jaruma a masana’antar ta Kannywood Hadiza Ali Gabon ta sanya da Rakiya Moussa a dandalinta Na Hadiza Gabon inda a cikin zantawar akai mata tambaya akan soyayyar.
Wannan tambayar tasa jarumar kuka share share inda ta bayyana irin son da take wa jarumi kaman haka.
Na Kamu Da Kaunarsa Ta Yadda Idan Na Tsaya Da Wani Saurayin Sai Na Ga Kamar Shine Ya Zo Wurin, Sai Na Yi Sauri Na Tafi Gida. Na Kamu Da Kaunarsa Ta Yadda Har Na Mutu Ba Zan Iya Warkewa Ba.
Sai dai da yawan mutane sun bayyana wanda take wa wannan soyayya wadda har wasu daga cikin masana’antar sun san haka wato Hamisu Breaka.