Labarai
Wani matashi ya labarta yadda ya Rasa Maryam bayan sunyi alkawarin Aure da ita.
Yadda Na Rasa Maryam Bayan Mun Yi Alkawarin Aure Da Ita
Daga Sirajo Sani, Sokoto
Wannan ita ce nake burin aure. An yi mana baiko a cikin watan Agustar 2022. Mun hadu a jami’ar Usmanu Danfodio Sokoto, Ina aji hudu a sashen tarihi, yayin da ita kuma take aji daya a fannin ilmin lissafi.
Mun yi alkawarin idan Allah ya nuna min na gama hidimar kasa za mu yi aure, na gama lafiya a jihar Nasarawa, na dawo gida. Ita kuma Allah ya yi mata rasuwa.
Ban san yadda zan kwatanta rashin ta a gare ni ba. Saidai na bar wa Allah komai domin shine mai cikakken iko. Allah ya gafartawa Maryam Ibrahim ka ya yi mata rahama.