Advertising
Advertising
Labarai

Dan wasan kwallon kafa na Super Eagles Ahmad Musa ya karya farashin man fetur a Kano lita ta koma N580

Dan wasan kwallon kafa na Super Eagles Ahmad Musa ya karya farashin man fetur a Kano lita ta koma N580

A lokacin da mutane suke wayyo Allah
da tsadar rayuwa musamman farashin man fetur, sai aka ji Ahmad Musa ya kawo sa’ida.

Advertising

A yau Litinin aka ji samu labari dan wasan
kwallon kafan Najeriya na Super Eagles Ahmed Musa ya rage farashin man fetur a gidan mansa.

Ga wadanda suke zaune a garin Kano zasu iya zuwa gidan man dan kwallon domin su sha fetur a kan N580 kasa da farashin gwamnati.

Maganar da muke yi ana saida litar man fetur a mafi yawan gidajen man garuruwan Arewacin Najeriya ne tsakanin N617 da N620.

Advertising

Ahmad Musa ya bada sanarwa a shafinsa na Twitter cewa ya zabi ya karya farashin a gidan mansa da ke hanyar Zariya a unguwa uku a Kano.

Ahmad Musa: “Fetur a kan #580 a gidan mai @MYCA -7a Kano.”

Tuni mutane su ka shiga yi wa dan kwallon Kafan ruwan addu’o’i na wannan taimako da ya yi a sa’ilin da fetur ke neman ya gagari talakawa.

Mazauna Legas sun yi mamakin irin wannan rahusa na tauraro kuma dan kasuwan.

Wannan ya sa aka ji wata salama Naziru ta na rokon ‘dan wasan ya taimakawa Gombawa da Sakkatawa da wannan rangwame na shi.

Masu bibiyar dandalin Twitter kuwa babu abin da su ke yi sai jinjinawa attajirin, ana yi masa addu’a Ubangiji ya kara masa dukiya mai yawa.

Nan da nan mutane suka fara tofa albarkacin bakin su, ga kadan daga ciki.

Engr. Fahad Shehu ya rubuta: “Allah ya saka maka da alheri. Yayi ma rayuwar
ka da ta iyalanka albarka. Allah ya jikan
mahaifanka, Ya saka su aljannar firdausi. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.”

Wani Bawan Allah ya ce a kan N640 su ke sayen lita a gidajen mai. Kafin a iya cika tankin karamar mota, sai an kashe fiye da N30, 000.

Shi kuwa Malam Shehu Liman Bana ya ce su na alfahari da wannan Bawan Allah.

Advertising
Back to top button