Advertising
Advertising
Labarai

Har yanzu dai mawaki Davido yana fuskartar fushin musulmai kan yin waka ana tozarta Sallah

Har yanzu dai mawaki Davido yana fuskartar fushin musulmai kan yin waka ana tozarta Sallah

Mawakin kudu Da aka fi sani da Davido tun jiya yake samun matsin lamba gami da tofin Alatsine kan wani abu da yayi da ake danganta shi da cin zarafin Addini gami da wulakanta salla.

Advertising

Koda yake Davido ba shine yayi abun ba amma ya shafawa kan sa kashin kaji gami da kunnen uwar shegun da yayi game da kiraye kirayen da ake masa kan lamarin yasa yafi mai kora shafawa.

Domin kuwa wani mawaki ne mai tasowa yayi wata waka inda a bidiyon wakar aka ga wasu na salla da wasun su ma ba musulmai bane suna cikin sallar kuma sai suka buge da rawa abin da kowanne musulmin kwarai ya gani sai zuciyar sa ta sosu.

Davido ya wallafa wannan bidiyo a shafin sa yana tallata wakar wanda kuma tun bayan da ya wallafa ake ta kiran sa akan ya sauke ta amma yaki hakan yasa duk wata kafa ta sada zumuntar musulmi ke masa zanga zanga ana ta wallafa hoton sa da
la’antar sa gami da kira ga musulmi da su fice daga cikin mabiyan sa wanda kawo yanzu shafin nasa ya samu ragin akalla kusan mabiya dubu dari biyu.

Advertising

Sai dai a yayin da ake wannan wasu daga mabiya addini daya da Davidon na ta maida martani kan cewa, wani mawakin Kudu mai suna Asake wanda ya
Akasance Musulmi ne shima yayi wata waka a coci har da akuya ya shiga chochin amma ba’a la’ance shi ba sai Davido wanda ake musu martanin yadda muka daukaki Addinin mu su ai ba haka sukawa
nasu ba da fatan Allah ya daukaka musulunci.

Domin kuji karin bayani a bidiyon da tashar Tsakar gida ta wallafa a shafinsu na Youtube, sai ku kalli bidiyon da muka sanya muku a kasa.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Advertising
Back to top button