Advertising
Advertising
Labarai

Yanzu yanzu: Jarumi Ali Nuhu ya godewa mawaki Davido kan goge bidiyon batanci ga Musulinci

Yanzu yanzu: Jarumi Ali Nuhu ya godewa mawaki Davido kan goge bidiyon batanci ga Musulinci

Awanni kadan bayan sukar Davido akan
bidiyon da ya daura, Ali Nuhu ya sauya tunani tare da ba wa mutane hakuri, Ali Nuhua shafinsa na Instagram ya godewa Davido saboda goge bidiyon da ya yi wanda ya jawo suka daga mutane.

Advertising

Ali Nuhu ya roki magoya bayansa da sauran Musulmi da su yi hakuri kada aci gaba da zage-zage don samun zaman lafiya.

Jarumin Kannywood, Ali Nuhu na daga cikin wadanda suka kirayi mawaki Davido da ya goge bidiyon da ya dake nuna rashin da’a ga Musulunci.

Ali Nuhu ya wallafa hoton Davido inda ya soki mawakin da cewa bidiyon ya sabawa Musulunci tare da bukatar goge bidiyon, Legit.ng ta tattaro.

Advertising

Bayan mawakin ya saduda tare da goge bidiyon, Ali Nuhu ya wallafa hoton Davido a shafinsa na Instagram inda ya yabi mawakin akan matakin da ya dauka.

Ya kuma roki magoya bayansa da sauran
Musulmi da su yi hakuri akan abin da ya faru don samun zaman lafiya.

A cewarsa: Mun gode daka goge bidiyon, duk wanda yaji zafin hakan yayi hakuri don zaman lafiya, bani da matsala da kowa.

Ina kira ga masoya na dasu guji dukkan wani abu da zai kawo zagi ko cin mutunci.

A wani bangare kuma jama’a sun soki jarumin da cewa bai kamata ya ba wa Davido hakuri ba.

toyin abraham cewa yayi: @realalinuhu mun gode dan uwa.

jamilu yakasai cewa yayi: Wannan abin kunya ne wallafa hoton Davido tare da gode masa, ba Davido bane ya cire
wannan bidiyon Instagram ne suka cire, ko da shi ya cire bai kamata ka gode masa ba.

tkannywood_fimmagazine: Goge bidiyon bai wadatar ba, ya kamata yaba da hakuri akan abin da ya aikata wasu suna cewa, ba shi ya goge ba kamfanin Instagram ne suka goge.

Shafin mutan__arewa suka ce: Goge wa kadai bai isa ba ya fito ya nemi afuwar Musulmai don bamu san waye ya goge
bidiyon ba.

maryam_ballah cewa tayi: Abin da yasa yake burgeni yana gyara kuskurensa, haka ake so dan adam ya zama, a nan gaba kada ya sake wasa da Musuunci saboda addini na akwai mutunci.

tagwayenasali suka ce: Ya kamata mu yaba masa tunda ya goge bidiyon, shi ne abin da ake bukata daman.

https://www.instagram.com/p/CvDmcl6qzsu/?igshid=NTc4MTIwNjQ2YQ==

Advertising
Back to top button