Labaran Kannywood

Jarumar masana’antar kannywood Hauwa Kakuri ta riga mu gidan gaskiya, Allah yayi mata Rasuwa

Jarumar masana'antar kannywood Hauwa Kakuri ta riga mu gidan gaskiya, Allah yayi mata Rasuwa

ALLAHU Akbar! A yau Lahadi Allah ya ɗauki ran jaruma a Kannywood, Hauwa Magaji Gwarzo.

‘Yar wasan, wadda aka fi sani da Mama Hauwa Kakuri, ta rasu ne a gidan ta da ke unguwar Kakuri Hausa, kusa da tsohuwar kasuwa, a Kaduna, sakamakon ciwon ciki da ta daɗe ta na fama da shi. An yi mata aiki a lokuta daban-daban har sau uku, a ƙarshe ya zama ajalin ta.

Malama Hauwa, mai kimanin shekara 55 a duniya, ta rasu ta bar ‘ya’ya 10 da jikoki tara.

An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a ƙofar gidan ta, daga nan aka kai ta gidan ta na gaskiya.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ‘yan fim, musamman na Jihar Kaduna, sun kaɗu matuƙa da rasuwar Hauwa Kakuri.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Al-Amin Ciroma, Alfazazee Muhammad, Sir Zeesu, Bilal M. Naseer, Abdul SD, Muhammad Showman, Ibrahim Maigala da Murtala Aniya.

Allah ya jiƙan ta da rahama, amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button