Labaran Kannywood

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta fara kama masu maganin gargajiya

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta fara kama masu maganin gargajiya

Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano, Alh. Abba El-Mustapha ya jaddda aniyar sa ta kawo tsafta tare da gyara a bangaren masu tallan maganin gargajiya duba da yadda wasun su ke yada kalaman batsa da hotunan da basu dace ba da nufin tallata magungunan su dan su ja hankalin masu saya

Alh El-Mustapha ya Kara da cewa shugabancin sa ba zai zubawa wannan halayya ido ta cigaba da faruwa a cikin alumma ba, Sabo da hakan ya Saba da tarbiyar Jahar Kano tare da koyarwar addinin Musulinci.

Abba na yin wannan jawabi ne a gaban harabar hukumar tace Fina-finan ta Jahar Kano jim kadan bayan kammala aikin kaman masu maganin gargajiyar da aka samu da laifin Saba dokar hukumar a wani aikin hadin gwiwa data gudanar tsakanin jami’an Yan sanda da ma’aikatan hukumar tace Fina-finan ta Jahar Kano.

Alh. El-Mustapha yace doka ce tabawa hukumar damar gudanar da wannan aiki a dan haka hukumar zata yiwa dokar biyayya sau da kafa domin cimma nasarar da tasa a gaba.

Indan ba a mantaba sati biyu da suka gabata, hukumar ta soke lasisin gudanar da aiki ga dukkannin abokan huldar ta, sannan tace har Sai ta tantance su tare da basu damar cigaba da aiki ciki ko harda Kungiyar masu tallan maganin gargajiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button