Labarai

Allahu Akbar yadda Dahiru Aliyu Dahiru yanada wasiyya Kafin mutuwar sa akan littafansa.

Kullum ina kallon litattafaina ina tunanin na rubuta wasiyyar inda za a kaisu idan na mutu don ba na son su kare a kasuwar tsofaffin litattafai.

So nake a ci gaba da karantasu har bayan mutuwata don haka nake tunanin rubuta wasiyyar a kaisu wani public library idan har yaya ko yan uwa ba za su karanta ba. So nake na haramta siyar da su.

Rayuwar nan ba ta da tabbas. Kana mutuwa za a manta da kai, don haka gwara ka bar abin alkhairi. Wasu ko RIP din ba za su rubuta ba. Wasu kuwa daga sun ce innalillahi wa inna ilaihi rajiun sai su saka headphones dinsu su ci gaba da jin wakar Davido ko Ado Gwanja. Shikenan sun manta da kai. Sai dai su shiga TikTok su ga comedy su yi dariya.

Ana gama kukan binneka kuwa za a fara tunanin raba gadonka. Watakila ma wani da bai taba taimakonka a rayuwa ba shi ne zai tayar da rigimar cin gadonka. Kowa sai ya manta da kai. Har matarka da yayanka sai sun manta da kai sun ci gaba da rayuwarsu. Duniya kuwa da ma ba zata tsaya ba.

Ka tsaya ka yi aiki nagari kuma ka barwa duniya abin alkhairi. Kada ka cuci kowa don ka gina rayuwar yayanka ko iyalinka. Karshe mutuwa za ka yi su cinye kudin kai kuma ka je lahira ka daku. Wasu ko wasiyyarka ba za su dauka ba. Su dai kawai su ci dukiyarka. To don me za ka ci dukiyar wasu ka gina rayuwar wadanda mantawa za su yi da kai?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button