Advertising
Advertising
Education

Hanya mafi Sauki da zaka dakatar da Bankin ka bayan an sace maka waya Saboda barayi.

Abu ɗaya da yakamata kasani cewa masu kwacen waya sunfi damuwa da sim card dinka fa, akwai wasu dake gefe wadanda da zarar an saci wayarka to su sim card din suke buqata Saboda su kwashe maka dukiyarka dake bankinka, Saboda ansan dai duk taqamarka shine ace kana da kudi a banki.

Advertising

Kana ankarewa an sace maka waya to kada ka tsaya tunanin wani kiran bankinka ko zuwa banki cikin gaggawa, domin idan kiransu zakayi kafin su ɗaga kuyi magana tunin anyi maka abinda za’ayi.

Haka ma idan zuwa zakayi nan ma kafin kaje ka shiga cikin bankin anyi abinda za’ayi.

Hanya mafi sauqi shine ka ari wayar wani dake kusa dakai domin toshe bankinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga, ina nufin da kanka zaka iya kulle account dinka ta yadda kuɗi ba zai fita ba sai dai ya shiga.

Advertising

Kusan kowanne banki akwai hanyoyin toshewar kada kuɗi ya fita, ga jerin bankunan da hanyar toshewar:

 1. Zenith Bank: * 966 * 911 #
 2. Access Bank: * 901 * 911 #
 3. GTB Bank: * 737*51* 74 #
 4. First Bank: * 894* 911 #
 5. WEMA Bank: * 945 * 911 #
 6. Key Stone Bank: * 7111* 911 #
 7. FCMB Bank: * 329* 911 #
 8. UBA Bank: * 919 * 911 #
 9. Sterling Bank: * 822 * 911 #
 10. Unity Bank: * 7799 * 911 #
 11. Fidelity Bank: * 770* 911 #
 12. Heritage Bank: * 745*7#
 13. Union Bank* 826* 911 #
 14. Ecobank* 326 * 911 #
 15. Polaris Bank * 833* 911 #
 16. Stanbic Bank * 909 * 911 #

Zaka iyayi a kowanne layi ba lallai sai layinka ba, kawai bayan kasaka account number zasu bukaci kasaka lambar da kakejin alert na wannan account din, shikenan zasu kulle kuɗi ba zai iya fita ba, duk randa kayi swap kuma to dole sai kaje bankinka sune zasu iya budewa komai yadawo yadda yake.

Allah ya tsaremu, a guji saka waya a aljihun gefe na riga ko aljihun gaban riga. Ka tabbatar wayarka tana inda ana kai hannu zakaji.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button