Advertising
Advertising
Uncategory

Rashin Masu Kishi A Arewa Ne Ya Sa Har Yau Abba Kyari Bai Dawo Aiki Ba.

DAGA Umar Abubakar Sarki

Advertising

Rashin wakilci na manyan Arewa da Sarakuna da kungiyoyin mu yasa har yau abba kyari bai dawo bakin aiki ba.

Yankin Inyamurai sun san cewa babu irin laifin da kanu bai ma gwamnati ba, kama daga kone kayan gwamnati zuwa kashe jami’an ta da duk miyagun laifuka, amma hakan bai hana manyan su daga ciki har da tsohon minista, suyi takakka xuwa villa dan rokawa kanmu afuwanshugaban kasa ba.

Sai gashi mu namu yankin da yake fama da matsalar tsaro, zai wahala a kwashe awanni 24 ba kaji labarin kisan wasu mutane ko sace wasu mutane ba, dan sandan da yafi kowa gaskiya da aiki a zahiri, dan sandan da hanyar Abuja zuwa kaduna da wasu sassa na kasan nan yayi kaurin suna wajan yakar yan ta’adda abba kyari an masa sharri an dakatar da shi, yanzu tsawon watanni a kalla ya kusa biyar kenan ko ma yafi amma baya bakin aiki.

Advertising

Dan sandan da tun da aka tsaida shi, babu wanda zai gaya maka takamai-mai wani aiki yanzu IRT take yi, ni in ka tambaye ni sunan shugaban ta ma ban sani ba, yanzu haka kuke so mu cigaba da rayuwa!!!

Yaushe ne zamuyi abun da ya dace? Duba yadda gidajen jaridu sukai ta zuzuta maganar abba kyari, duba yadda yanzu aka kama aminin turji amma duk sunyi shiru.

Allah ka kawo mana agajin ka, ya Allah ka bamu zaman lafiya!!!

Advertising

One Comment

  1. Gaskiya bawan allah ya fada wannan abu da ake a nigeria sai dai muce allah saka mana wlh shugabanni ba su yarda da ranar tsayu ba tunda suke aika ta wannan lf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button