Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wani boka ya durkawa wata budurwa ciki a jihar Bauchi

Jami’an Yan Sanda jihar Bauchi sunyi nasara kama wani boka da ake zargi da yaiwa matar aure ciki yayin da ta kai ‘yarta fomin yimata magani.

Advertising

SP Ahmad Muhammad Wakili Ya ce mutumin da ake zargi dan kimanin shekaru 32 na Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Yayi anfani da kayan maye wajen yin amfani da yariyar kafin yay mata fade.

Mai magana da yawun rundunar ya kuma ce sun kama wani malamin makaranta mai kimanin shekara 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekara bakwai fyade a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Ya ce, “Bayanan da ’yan sanda suka tattara sun nuna cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Ajiya a garin na Alkaleri, malami ne a wata makaranta mai zaman kanta a garin.

Advertising

Ma’aikatan namu sun kuma kama wani mai sayar da askirin a garin na Bauchi, saboda zargin yin luwad* ga wani yaro mai shekara 12 a bayan wani banki.

“Binciken farko-farko ya nuna wanda ake zargin ya sayi ruwan leda ne daga hannun yaron, sannan ya yaudare shi zuwa cikin wani shago ya yi lalatar da shi a ciki,” inji Kakakin ’yan sandan. (NAN)

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button